Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia : Yahya Jammeh ya amince ya mika mulki

Shugaba Adama Barrow da ya lashe zaben kasar Gambia ya ce Yahya Jammeh ya amince ya mika masa mulki sannan ya bar kasar.

Yahya Jammeh ya sauka daga mulkin Gambia.
Yahya Jammeh ya sauka daga mulkin Gambia.
Talla

Zababben shugaban na Gambia ya sanar cewar Jammeh ya amince yanzu ya  mika masa ragamar mulki sannan ya bar kasar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a wannan juma'ar a daidai lokacin da al'umma a ciki da wajen kasar suka zuba ido dan ganin yadda za ta kaya a kokarin da ake na ganin Jammeh ya mika mulki cikin ruwan sanyi.

A baya can shugaban hukumar kungiyar kasashen yammacin Afirka Marcel Alain de Souza, ya shaida wa wani taron manema labarai cewa a wannan juma’a ne za a bai wa Jammeh dama ta karshe .

Senegal da wasu kasashen Afrika ma dai sun tura dakarunsu Gambia a yammacin jiya Alhamis bayan da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da kudurin da ke bai wa kasashen yammacin Afirka damar yin amfani da karfi soji akan Yahya Jammeh.

Kungiyar Tarayyar Afrika ta ce Sojoji za su afkawa Gambia idan har Yahya Jammeh ya ki amincewa ya sauka bayan tattaunawa da Alpha Conde sai dai ga dukkan alamu za'a iya cewa yanzu kwaliya ta biya kudin sabulu ganin Jammeh ya fice daga kasar ba tare da wani tashin hankali ba.

Al'ummar kasar fiye da dubu 45 ne suka tsere daga kasar gudun barkewar rikici bayan da Jammeh ya dage kan ci gaba da mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.