Isa ga babban shafi
Gambia

Yahya Jammeh ya ki sauka bayan cikar wa’adin mulkin shi

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya ki sauka daga karagar mulki duk da barazana da ya ke fuskanta daga Senegal da kasashen ECOWAS na yin amfani da karfi domin kawar da shi bayan cikar wa’adin mulkin shi.

Yahya Jammeh, ya kafa dokar ta baci domin ci gaba da mulki a Gambia
Yahya Jammeh, ya kafa dokar ta baci domin ci gaba da mulki a Gambia MARCO LONGARI / AFP
Talla

A yau ake sa ran rantsar da Adama Barrow a Senegal wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Disemba.

A jiya Laraba ne 18 ga watan Janairu wa’adin mulkin Jammeh ya kawo karshe, kuma ya ki sauka bayan ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da ya sha kaye.

Dakarun Afrika yanzu haka na shirin yin amfani da karfi domin dora Adama Barrow kan mafadan ikon Gambia.

Senegal ta ba Jammeh zuwa 12 na daren jiya ya sauka, bayan ta jibge dakarunta a kan iyakokin Gambia.

Mataimakiyar shugaban kasar Gambia Isatou Njie-Saidy ta yi murabus kafin cikar wa’adin Jammeh , kuma yanzu ministocinsa 6 ne suka yi murabus domin nuna rashin goyon bayansu ga zarcewar wa’adin mulkin shi.

Fargabar yaki ya sa daruruwan mutanen Gambia ne tserewa zuwa Senegal kamar yadda baki ‘yan kasashen waje da suka je yawon bude ido ke ficewa kasar.

Daga yau dai za a iya samun gwamnati biyu a Gambia bayan rantsar da Adama Barrow a ofishin jekadancin kasar a Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.