Amurka ta kashe mayakan IS 80 a Libya
Sama da mayakan ISIL 80 ne jirgin yakin Amurka ya hallaka a sansaninsu da ke Libya, cikinsu akwai wadanda suke da hannu a shirya hare-haren ta’addanci da aka kai a wasu sassan kasashen Turai kamar yadda fadar gwamnatin Amurka ta Pentagon ta sanar.
Wallafawa ranar:
Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter ya ce tabbas wadannan mutane suna kan shirya kaddamar da harin ta’addanci a Turai, Carter ya sanar da hakan ne a yayin da ya rage ‘yan sa’o’i ya bar aiki karkashin gwamnatin shugaba Barack Obama.
Kafin jiragen yakin Amurka su kaddamar da harin a maboyar mayakan da ke kudancin birnin Sirte an hango Su dauke da makamai suna gudanar da atisaye a sansanin na su.
Kafin daren laraba a kai harin kan mayakan na ISIL da ke barazana ga zaman lafiya a kasar ta Libya da ma sauran kasashen da ke makwabtaka da ita, kakakin ma’aikatar tsaron Amurka Peter Cook ya ce an sami gagarumar nasara a harin da aka kai kan mayakan
Amurka dai ta kai harin ne bisa umarnin shugaba Barack Obama mai barin gado tare da hadin-gwiwar gwamnatin hadakar Libya
Ana ganin nasarar kashe mayakan har 80 zai karya lagonsu na kai sabbin hare-hare kan dakarun kasar da ma fararren hula da ke aiki ba dare ba rana a kokarin samar da zaman lafiya a birnin na Sirte.
Libya ta fada cikin tashin hankali bayan rikicin juyin juya hali da ya kawo karshen mulkin marigayi kanar Ghadafi a shekarar 2011, tun daga wannan lokacin mayakan ISIL suka mayar da kasar mabuyarsu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu