Isa ga babban shafi
Najeriya

An kai harin bom a Jami’ar Maiduguri

Hukumomin tsaro a Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutane hudu sakamakon harin da aka kai a sanyin safiyar yau litinin a cikin harabar jami’ar garin Maiduguri da ke jihar Borno, kuma daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da wani mashahurin Shehin malami Farfesa Aliyu Usman Mani.

Masallacin Jami'ar Maiduguri da aka kai harin kunar bakin wake
Masallacin Jami'ar Maiduguri da aka kai harin kunar bakin wake RFI Hausa/Bilyaminu
Talla

Wakilin RFI Hausa Bilyaminu Yusuf ya ce harin kunar bakin wake ne aka kai inda mace da namiji suka tada bom din da ke jikinsu a cikin Masallacin gidajen Malamai da kuma kofar shiga Jami'ar.

Dan kunar bakin waken na farko ya shiga masallaci ne a cikin jami’ar inda ya tayar da bom.

‘Yar kunar bakin waken mace kuma ta yi kokarin shiga kofar jami’ar ne gate 5, tana kokarin haurawa wani jami’i ya harbe ta sai bom din ya tashi.

Wannan shi ne karo na farko da aka taba kai harin bom a cikin Jamiar Maiduguri.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.