Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta bukaci a saki Zakzaky

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta bi umurnin kotu ta saki jagoran Shi’a Ibrahim Zakzaky da daruruwan mabiyan shi da ake tsare da su.

Kusan shekara guda ana tsare da jagoran Shi'a a Najeriya
Kusan shekara guda ana tsare da jagoran Shi'a a Najeriya AFP PHOTO PIUS UTOMI EKPEI
Talla

A yau ne wa’adin kwanaki 45 da kotun Abuja ta ba gwamnati zai kawo karshe.

Daraktan Amnesty a Najeriya Makmid Kamara ya ce hakan zai tabbatar da gwamnati ta raina doka idan har ta yi watsi da bin umurnin kotu.

Zakzaky ya shafe tsawon shekara guda a tsare tun lokacin rikici tsakanin mabiyan shi da Sojojin Najeriya a Zaria.

‘Yan Shi’a sun ce an kashe ma su mambobi akalla 350, alkalumman da sojojin Najeriya suka musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.