Isa ga babban shafi
Nijar

‘Yan Boko Haram 50 sun mika wuya a Diffa

Mahukunta a jahar Diffa a Jamhurriyar Nijar sun ce wasu mayakan kungiyar Boko Haram kusan 50 ne suka mika wuya, kuma Talatin daga cikinsu sun soma bayyana shirinsu na tuba tare da mika makamansu.

Sojojin Nijar da ke fada da Boko Haram a Diffa
Sojojin Nijar da ke fada da Boko Haram a Diffa Nicolas Champeaux pour RFI
Talla

Daga baya ne sauran ashirin suka rungumi shirin na zaman lafiya.

Jahar Diffa dai ta sha fama da ayyukan kungiyar Boko Haram inda rayukan mutane da dama suka salwanta baya ga tarin dukiya sakamakon hare-haren mayakan.

Mousa Aksar dan jarida a Nijar ya ce da kansu ‘Yan Boko Haram suka mika wuya ga sojojin Nijar da ke fada da su a Diffa.

Sai dai kuma Mutanen Diffa na son hukumomin Nijar su tabbatar da tubar gaskiya mayakan suka yi kada daga baya su aibatawa mutane.

An dai samar wa mayakan wani sansani da za a ba su horo na gyara halayensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.