Isa ga babban shafi
Kamaru

Kamaru ta sanar da samun nasara akan Boko Haram

Gwamnatin Kamaru ta ce dakarunta sun yi nasarar murkushe Boko Haram a iyakokinta da Najeriya bayan kashe mayakan kungiyar da dama tare da kubutar da mutanen da suke garkuwa da su.

Sojojin Kamaru da ke fada da Kungiyar Boko Haram ta Najeriya
Sojojin Kamaru da ke fada da Kungiyar Boko Haram ta Najeriya AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Tun a watan Disemba Kamaru ta kaddamar da farmaki akan Boko Haram bayan gwamnatin Najeriya ta sanar da murkushe mayakan kungiyar daga Dajin Sambisa.

Kakakin gwamnatin Kamaru Issa Tchiroma Bakary ya ce sojojinsu sun kashe ‘Yan Boko Haram kimanin 100 a makwannin da suka gabata, tare da kame wasu 30 da yanzu haka ake tsare da su a gidan yari.

Sai dai kuma har yanzu Boko Haram na ci gaba da yin barazana a arewacin Kamaru inda a ranar Laraba wasu matasa da ‘Yan Mata guda biyu suka kai harin kunar bakin wake. Kodayake maharan ne kawai suka kashe kansu.

Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya na cikin rundunar hadin guiwa da ke yaki da Boko Haram da suka addabi Yankin Arewa mai nisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.