Isa ga babban shafi
Afrika-tafkin Chadi-Najeriya

Mata na fadawa karuwanci a yankin tafkin Chadi-Red Cross

Kwamitin bada agajin gaggawa na duniya, Red Cross, wanda aka fi sani da ICRC a takaice, ya ce mafi akasarin mata a yankin tafkin Chadi sun fada karuwanci ba bisa son ransu ba domin kula da kansu da kuma ‘ya’yansu.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a yankin Tafkin Chadi, da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu
Wasu daga cikin 'yan gudun hijira a yankin Tafkin Chadi, da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu
Talla

Cikin wani rahoto da kwamitin na ICRC ya fitar, ya danganta halin da matan suka tsinci kansu da ta’addancin kungiyar Boko Haram, wadda ta yi sanadiyyar raba akalla mutane sama da miliyan 2.4 da gidajensu, wadanda a yanzu ke rayuwa a yankin na tafkin Chadi.

Simon Brooks, shi ne shugaban tawagar kwamitin na Red Cross a kasar Kamaru, ya ce a bayyane ta ke yadda kananan yara basa samun isassehn abinci mai gina jik, a yankin.

Brooks ya kara da cewa hakan ya tilastawa mata da ke da yara a karkashinsu, yanke shawarar shiga karuwanci, domin samun abinci, kasancewar rayukan mazajen da damansu, sun salwanta sakamakon rikicin Boko Haram.

Simon Brook ya ce wani abin tashin hankali shi ne yadda yakin da ake cigaba da gwabzawa a kasashen Syria da Iraqi ya dauke hankalin duniya daga kan halin da ake ciki a yankin tafkin Chadi.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce sama da mutane miliyan 7 ne basa samun isasssahen abinci a yankin na tafkin Chadi, a gefe guda kuma fargabar rashin cikakken tsaro yasa kungiyoyin agaji gaza kai daukin da ake bukata a yankin.

Zalika rahoton Majalisar ya ce akalla kananan yara rabin miliyan ne ke fama da yunwa, sakamakon rashin abinci mai gina jiki, kuma muddin ba’a kai musu agajin ba za’a samu hasarar rayuka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.