Isa ga babban shafi
Chadi

Chadi ta rufe kan iyakarta da Libya

Chadi ta sanar da rufe kan iyakarta da kasar Libya saboda tsaro daga barazanar ‘yan ta’adda da kan iya kutse a cikin kasar. Sai dai Chadi ba ta fayyace ‘Yan ta’addar da ta ke nufi ba.

Taswirar kan iyakar Chadi da Libya
Taswirar kan iyakar Chadi da Libya (Carte : RFI/P. Biancarelli)
Talla

Firaministan Chadi ne Albert Pahimi Padacket ne ya sanar da daukar matakin a jawabin da ya gabatarwa ‘yan kasar ta kafar Radio da Talabijin na gwamnatin.

Firaministan ya ce gwamnatin ta dauki matakin domin barazanar da ta ke fuskanta ta kwararar ‘yan ta’adda daga kan iya tsallakowa cikin Chadi daga kudancin Libya.

Chadi ta rufe iyakar ne a yankin Tibesti yanki mai cinkoson jama'a ‘yan kabilar tubawa da ke rayuwa a kan iyaka da Libya.

Kasar Chadi na kan gaba a yaki da ta’addanci a Afrika inda Sojojinta ke samun goyon bayan Amurka da Faransa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.