Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 19/10 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 19/10 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 19/10 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/10 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/10 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 18/10 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 18/10 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 14/10 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 14/10 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 18/10 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Afrika

Habasha ta yi wa Fursunoni dubu 10 afuwa

media Al'ummar yankin Oromia da ke kin jinni gwamnatin Habasha REUTERS/Tiksa Negeri

Gwamnatin Habasha ta bada umarnin sakin fursunoni dubu 10 da aka kama a yankin Oromia na kasar, da ya yi fama da zanga-zangar kin gwamnati. Sai dai kuma masu adawa da gwamnatin sun ce har yanzu ana tsare da wasu dubban ‘yan yankin.

Fursunonin da aka saki sun hada da tsofaffi, masu fama da rashin lafiya da kuma wadanda ke da yara kanana, sai dai kuma ba a kai ga tantance ko mutanen na daga cikin wadanda aka kama bayan kafa dokar ta baci da gwamnatin Habasha ta yi a yankin na Oromia ba.

Sai dai a cewar kakakin ‘yan adawar kasar, Mualtu Gemechu, har yanzu akwai ‘yan yankin na Oromia sama da 60,000 da gwamnatin ke ci gaba da tsarewa.

Mista Gemechu ya ce kasancewar fursunonin sun fi karfin gidajen yarin kasar, a yanzu an koma tsare da dama a bayan gari.

A watan Oktoban shekara ta 2016 ne gwamnatin Habasha ta kafa dokar ta baci a yankin Oromia, bayan gagarumar zanga-zangar nuna kin jinni gwamnati kan yadda aka ware su daga shiga al’amuran kasar kama daga siyasa da tattalin arziki.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure