Isa ga babban shafi
Mali

An fadada binciken Bafaransar da aka sace a Mali

Dakarun Mali da takwarorinsu na Faransa sun fadada bincike domin kubutar da wata ma’aikaciyar agaji Bafaransa da aka sace a garin Gao da ke arewacin Mali.

Sojojin Faransa a yankin Gao na Mali
Sojojin Faransa a yankin Gao na Mali RFI/David Baché
Talla

A ranar Asabar ne aka sace ma’aikaciyar agajin mai suna Sophie Petronin a garin Gaoh da ke arewacin Mali.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka tana aiki kafada da kafada da hukumomin Mali domin ceto matar da ta share tsawon shekaru 20 zaune a yankin.

Kader Toure, shugaban wani gidan rediyo mai zaman kansa a Gao ya ce Sophie mace ce da ta shaku sosai da birnin.

Sophie na aikin taimaka wa jama’a a fage da dama musamman kula da yara da ke fama da karancin abinci mai gina jiki da sauran ayyuka na kiwon lafiya.

Ana tunanin dai mayakan kungiyar Al Qaeda reshen Afrika ne suka sace Bafaransar a Gao.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.