CPJ ta gargadi Kamaru kan musguna wa 'yan jaridu
Kungiyar da ke sa ido kan ayyukan ‘yan jaridu a duniya ta gargadi kasar Kamaru kan yadda ta ke hana ‘yan cin fadin albarkacin baki da kuma musgunawa ‘yan jaridu.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta CPJ ta ce, a kwanan nan hukumomin Kamaru sun cafke wani dan jarida da ke daukan rahoto kan wata zanga-zanga, yayin da kuma suka dakatar da kafafan yada labarai da suka hada da gidajen rediyo da talabijin, baya ga sanya takunkumi kan wasu ‘yan jaridun da dama.
Wakilin kungiyar a yammacin Afrika Peter Nkanga, ya bukaci hukumomin na kasar da su gaggauta sakin wakilin gidan rediyon Faransa, Ahmad Abba.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da hukumomin kasar ke shirin gurfanar da Abba a gaban kotun soji a ranar 4 ga watan Janairu mai zuwa kan zargin alaka da Boko Haram, amma har yanzu an kasa gabatar da sheda akan haka.
Tun a ranar 30 ga watan Julin shekarar 2015 ne, aka kama wakilin na sahen hausa na RFI.
A bangare guda, ‘yan jaridun Kamaru sun bayyana cewa, a farkon wannan watan ne, gwamnatin kasar ta kuma haramta wa kafafan yada labarai masu zaman kansu, watsa muhawarar siyasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu