Isa ga babban shafi
Gambia

Ziyarar sasanta rikicin kasar Gambia

Tawagar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ECOWAS  ta isa a birnin Banjul na kasar Gambia, domin shawo kan shugaba Yahya Jammeh da ya mika ragamar mulkin kasar a hannun wanda al’umma ta zaba.

Saliyo da Liberia na daga cikin kasashen Afrika da ke son sasanta rikicin kasar Gambia
Saliyo da Liberia na daga cikin kasashen Afrika da ke son sasanta rikicin kasar Gambia REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Tawagar dai ta kunshi shugabar Liberia Ellen Johnson, da na Najeriya Muhammadu Buhari, da shugaban Saliyo Ernest Ba Kuruma da kuma shugaban Ghana mai barin gado John Dramani Mahama.

Shugaban hukumar kungiyar ta Ecowas Marcel Alain de Souza, ya ce da farko za su jarraba hanyoyi na diflomasiyya, idan an gaza, akwai yiyuwar za a yi amfani da karfin soji.

Rahotanni daga kasar na cewa jami’an tsaro sun kwace ikon babban ofishin hukumar zaben kasar ta Gambia.

Ranar daya ga watan Disamba aka gudanar da zaben shugabancin kasar da ya bai wa Adama Barrow na jam'iyyar adawa nasara kuma jim kadan da bayyana sakamakon zaben shugaba mai ci Yahya Jammeh ya meka sakon taya murna ga Barrow.

Rikicin da ke kunno kai ba ya rasa nasaba da matakin da shugaba Jammeh ya dauka na tande amansa ganin yadda rana tsaka ya soma kalubalantar sakamakon zaben.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.