Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

ICC zata binciki Afrika ta Kudu bisa rashin kama shugaban Sudan

Kotun Hukunta manyan laifufuka ta sanar da cewar zata gudanar da bincike kan dalilin da ya sa kasar Afirka ta kudu taki kama shugaban kasar Sudan Omar Hassan al Bashir, da ake nema ruwa a jallo lokacin da ya ziyarci kasar.

Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma tare da Omar al-Bashir Shugaban kasar Sudan
Shugaban Africa ta Kudu Jacob Zuma tare da Omar al-Bashir Shugaban kasar Sudan
Talla

Alkalan kotun, sun bukaci bayanai daga babbar mai gabatar da kara Fatou Bensouda da kasar Afirka ta kudu da kuma Majalisar Dinkin Duniya kan batun, wanda ake saran zaman sauraro akai ranar 7 ga watan Afrilu na shekara mai zuwa.

Takaddama tsakanin Afrika ta Kudu da kotun ya sa kasar ta sanar da janye wakilcin ta.

A shekara ta 2010, kotun ICC ta zargi shugaban Sudan al-Bashir, da hannu cikin aikata kashe kashen da suka auku a Sudan ta Kudu, tare da umurtar kasashen da ke karkashinta su kamashi, sai dai hakan bata samu ba, kasancewar shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya kyale al-Bashir ficewa daga kasarsa, bayan kammala taron tarayyar Afrika da ya gudana a kasar, a waccan lokaci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.