Isa ga babban shafi
Sahel-Libya

'Kungiyar IS barazana ce a Yankunan Sahel'

Bayan kubucewar garin Sirte daga hannun mayakan IS, sakamakon fatatakarsu da dakarun gwamnatin kasar Libya suka yi, hadarin da ake fuskanta a halin yanzu shine yadda mayakan suka bazu a kasashen yankin sahel da ke makwabtaka da Libya.

Mayakan ISIL na bazuwa a Yankunan Sahel
Mayakan ISIL na bazuwa a Yankunan Sahel REUTERS/Stringer/Files
Talla

Ganin yadda lamuran suka tabarbare kan rashin wata tsayayyar hukuma, tare faduwar birnin Sirte yanzu haka kungiyar IS, ta tunkari wasu kasashen da ke yankin na Sahel al’amarin da ke nuna har yanzu akwai sauran zomo a kaba a wannan yanki.

Yankin kan iyakar kudancin kasar Libya dai, ya hada kasashe da dama na nahiyar Afrika.

Kusurwar Salvador mashigi ne mai tsaunuka, da ke da wahalar shiga inda bata gari ke ci gaba da baje kolinsu musaman ma kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A cewar masharhanta ayyukan ta’addanci yankin kusurwar ta Salvador, wani babban falale ne mai hamada da ya kaucewa zura idon jami’an tsaron kasashen da suke tarayya da shi, irin su Libya da Jamhuriyar Niger da Algérie, da ma tarayyar Nigeria.

Tun bayan faduwar gwamnatin shugaba Mouammar Kadhafi a 2011, sannau a hankali yankin kudancin kasar Libiya, ya zama wata babbar matattarar ‘yan ta’adda da ke ci gaba da safarar miyagun kwayoyi da makamai tare da bai wa mazauna yankin da talauci ke addaba cin hanci.

Yawan dakarun kungiyar ta IS da ke wannan yanki a halin yanzu sun kai dubu 5 a cewar wani nazarin kwararu, inda IS ke ci gaba da daukar zarata daga sauran mayakan kungiyoyin da ke dauke da makamai da suka rasa manufa.

A kullum kwararru na kashedi kan ci gaban da kungiyar ta IS ke samu a ko ina cikin yankin sahel a kudancin kasar Libya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.