Isa ga babban shafi
Ghana

Al'ummar Ghana na kada kuri'a a zaben shugaban kasa

Yau ake gudanar da zaben shugaban kasar Ghana, in da ake saran mutane miliyan 15 za su zabi shugaba tsakanin 'yan takara 7 da ke fafatawa da juna. Shugaba mai ci, John Dramani Mahama na fuskantar kalubale daga babban dan adawa Nana Akufo- Addo da wasu 'yan takara 5. 

Al'ummar Ghana na gudanar da zaben shugaban kasa a yau Laraba
Al'ummar Ghana na gudanar da zaben shugaban kasa a yau Laraba REUTERS/Luc Gnago
Talla

Da misalin karfe 7 agogon Ghana ne  aka bude tashoshin zabe a sassan kasar.

Shugaba Mahama mai shekaru 58 na neman wa’adi na biyu, yayin da Nana Akufo-Addo mai shekaru 72 ke neman raba shi da kujerar shugabanci a takararsa ta uku, bayan ya sha kaye sau biyu a baya.

Mahama ya kwashe ranar karshe na yakin neman zaben yana karade manyan yankuna uku da ake ganin suna da matukar tasiri da suka hada da Brong-Ashafo da Ashanti da Greater Accra, in da ya rika tikar rawa yana neman goyan bayan jama’a.

Akufo-Addo ya dade yana sukar Mahama kan yadda ya jefa kasar cikin matsalar tattalin arziki duk da arzikin man da ta samu.

Masu sa ido na kallon zaben a matsayin mai sarkakiya wanda kan iya zuwa kowanne bangare ganin yadda zabubbuka a Afirka ke bada mamaki 'yan shekarun nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.