Isa ga babban shafi
Gambia

Gambia na zaben Shugaban kasa

‘Yan kasar Gambia na gudanar da zaben shugaban kasa a yau Alhamis wanda shugaba Yahya Jammeh ke neman wa’adin shugabanci karo na biyar bayan shafe shekaru 22 kan karagar mulki.

Hukumar zaben Gambia na raba kayan zaben shugaban kasa zuwa runfunan zabe
Hukumar zaben Gambia na raba kayan zaben shugaban kasa zuwa runfunan zabe REUTERS
Talla

Za a bude runfunar zabe da misalin karfe 8 na safe agogon GMT, sannan za a kammala kada kuri’a da misalign karfe biyar na yamma.

‘Yan takara uku ne za su fafata a zaben da suka hada da Shugaba mai ci Yahya Jammeh da Adama Barrow dan takarar hadakar gungun jam’iyun adawa da kuma Mama Kandeh, wani tsohon dan majalisar dokokin jam’iya mai mulki, da ya tsaya a karkashin tutar wata sabuwar jam’iyya ta GDC.

Sai dai a wannan karon shugaban na fuskantar babban kalubale daga dan takarar hadin gwuiwar ‘Yan adawa Adama Barrow wanda ya sha alwashin kawo karshen shugabancin Jammeh.

Gambia dai na cikin kasashen da Ingila ta yi wa mulkin mallaka a yankin yammacin Nahiyar Afrika da ke makwabtaka da kasar Senegal da kuma gabar ruwan tekun Atlantika.

Kungiyar Amnesty International ta gargadi hukumomin kasar kan tabbatar da zaman lafiya bayan kammala zaben.

Rahotanni sun ce an toshe kafofin sadarwa na Intanet tun a jajibirin zaben, inda ake zargin hukumomin kasar da kokarin dakile hada gangamin ‘Yan adawa tare da haramta tattauna matsalolin zaben a kafofin sada zumunta na intanet.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.