Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

Afrika ta tsakiya na bukatar agajin gaggawa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na fuskantar agajin gaggawa saboda yadda rabin al’ummarta ke cikin matsanancin hali. Wannan ya sa Majalisar ta kaddamar da gidauniyar Dala miliyan 399 domin kai wa al’ummar kasar agaji.

Ziyarar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai jiran gado Antonio Guterres à Bangui
Ziyarar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya mai jiran gado Antonio Guterres à Bangui RFI/Pierre Pinto
Talla

Shugaban aikin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya a kasar, Fabrizio Hochschild ya ce shekarun da aka kwashe ana fama da talauci a kasar da kuma tashin hankalin da ya biyo baya sun jefa al’ummar Afirka ta tsakiya cikin mawuyacin hali.

Jami’in ya ce yanzu haka rabin al’ummar kasar na fama da tsananin yunwa, yayin da kashi 40 na yaran da ke kasa da shekaru 3 ke fama da tamowa a kasar da yaro guda daga cikin 5 ba ya kai wa shekaru 5 a raye.

Ministar kula da lafiyar al’ummar kasar Virginie Baikoua ta ce lalle idan ana bukatar zaman lafiya ya zama dole a magance matsalar yunwa.

A farkon watan nan masu bada agaji na duniya sun yi alkawarin bai wa kasar euro biliyan biyu domin taimakawa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.