An cafke Sarkin da ake zargi da tinzira ‘yan banga a rikicin Uganda
Yan Sanda a kasar Uganda sun kama Sarkin wata kabila da ake zargi da tinzira magoya bayan sa wajen haddasa rikicin da ya hallaka mutane 55.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun Yan Sandan Andrew Felix Kaweesi ya ce an samu barkewar fadan ne a garin Kasese lokacin da masu tsaron Sarkin mai suna Charles Wesley Mumbere na Masarautar Rwenzururu suka kai hari kan jami’an tsaron dake sintiri, inda suka kashe Yan Sanda 14, yayin da Yan Sandan suka kashe masu gadin Sarkin 41.
Kakakin Yan Sandan ya ce suna zargin Sarkin da jagorantar kungiyar ‘yan bangan da suka yi sanadiyar mutuwar yan sandan kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu.
Shugaban kasar ta Uganda Yoweri Museveni ya bukaci rusa kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu