Isa ga babban shafi
Madagascar

An kawo karshen taron kungiyar Francophonie

A karshen zaman taronta karo na 16 da ta gudanar a birnin Antananarivo na kasar Madagascar, taron da ya samu halartar shuwagabannin da dama daga nahiyar Afrika da na da sauran na sassan duniya.  Kungiyar ta yi kiran kasashen mambobinta, da su karfafa kyakyawar hulda  da nufin yaki da ayyukan ta’addanci.Za a iya cewa kasashen kungiyar ta francophonie na daga cikin kasashen da ayukan ta’adanci ya fi yi wa illa. 

Hoton shuwagabanin kasashe mahalarta taron Francophonie a Madagascar, le 26 novembre.
Hoton shuwagabanin kasashe mahalarta taron Francophonie a Madagascar, le 26 novembre. STEPHANE DE SAKUTIN / AFP
Talla

Babbar sakatariyar kungiyar uwargida Michaëlle Jean, a lokacin da take yiwa manema labarai bayani bayan rufe zaman taron tace doli ne sai an samu babban hadin guiwa da cudani in cudeka ta fuskar fasaha samar da kudade da kuma masayar bayanan sirri da suka dace tsakanin kasashe mambobin kungiyar, wanda hakan zai bada damar yaki da ayukan ta’addanci.

Shi kuma shugaban kasar ta Madagascar Hery Rajaonarimampianina, cewa yayi kasashe mambbbin kun giyar sun dau alkawali, musamman ta bangaren da ya shafi tsaro. Ya kuma ce, sun hakkake cewa, sai an samu ci gaban tattalin arziki ake iya tabbatar da zaman lafiya da daidaito a duniya

Shugaban kasar Fransa François Hollande, da ya halarci buda zaman taron a ranar assabar da kuma bai samu damar halartar rufe shi ba a yau lahadi kira yayi da cewa ya kamata kasashen na Francophonie su karfafa huldarsu wajen yaki da tsatsauran ra’ayin musulunci a cikin fadin kasashen kungiyar.

Inda ya ce ba su da yancin yin watsi da matasan ksashen nasu ba tare da samar masu da mafita ba, su barsu sakaka, karerayin da kungiyoyi 'yan tsatsauran ra’ayi su ci gaba da fasa masu kanu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.