Burkina Faso-Cote D'Ivoire
Cote D'Ivoire ta mika wasu Sojoji zuwa Burkina Faso
Hukumomin kasar Cote D’ivoire sun tisa keyar wasu mayan hafsan sojan kasar Burkina Faso zuwa gida, sojojin da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki na watan Satumba shekarar 2015.
Wallafawa ranar:
Talla
Wadannan sojojin na daga cikin masu tsaron tsohon Shugaban kasar Blaise Compaore dake samu mafaka a kasar Cote D’ivoire yanzu haka.
Ministan cikin gida da kuma tsaron kasar Burkina Faso Simon Compaore ne ya sanar da haka bayan wata ganawa da hukumomin kasar Cote D’ivoire.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu