Sultani Makenga ya tsere daga Uganda
Kasar Congo ta tsaurara matakan tsaro da bincike a iyakokin kasar, sakamakon bacewar tsohon soji kuma jogoran kungiyar ‘yan tawayen M23 Sultani Makenga, da ake tsare da shi a Uganda mai makwabtaka da ita.
Wallafawa ranar:
Julien Paluku, Gwamnan Arewacin Kivu, ya ce sun dau matakan ne bayan hukumomin Uganda sun ce ba su da masaniyar inda Makenga ya shiga, tsohon jagoran ‘yan tawayen M23 a DR Congo.
Kafin cin karfin su a shekarar 2013, kungiyar M23, na daga cikin manyan kungiyoyin ‘yan bindiga da ke tada zaune tsaye a Congo duk da kawo karshan yakin basasa kasar tsakanin 1998-2003.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu