Isa ga babban shafi
Masar

Masu zanga zanga sun yi arangama da ‘yan sanda a Masar

Mutane 130 jami’an tsaro suka kama sassan kasar Masar, bayan bijirewa dokar haramcin gudanar da zanga zanga ba tare da izini ba, da gwamnatin kasar ta kafa.

Jami'an tsaro a Masar, da suka yiwa filin taro na Tahrir kawanya
Jami'an tsaro a Masar, da suka yiwa filin taro na Tahrir kawanya REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

An kama masu zanga zanga 39 a birnin Cairo, yayinda aka damke ragowar a sauran sassan kasar, hadi da amfani da barkonon tsohuwa da harsasan roba kan dandazon masu zanga zangar a yankin Beheira.

Wata kungiya mai rajin kare hakkin talaka ce ke amfanin da kafafen sadarwar zamani, wajen shirya zanga zangar, biyo bayan tashin farashin kayan abinci a kasar tare da adawa da gwamnatin Abdel Fata al-Sisi.

Tun bayan hambarar da mulkin Muhd Morsi da sojoji suka yi a shekara ta 2013, gwamnatin Masar ta haramta gudanar da zanga zanga ba tare da samun izininta ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.