Isa ga babban shafi
Masar

Asusun IMF ya bawa Masar bashin dala biliyan 12

Asusun bada lamuni na Duniya IMF ya amince da bawa Masar rancen kudi dala biliyan 12 na tsawon shekaru uku, domin magance matsalar tattalin arziki da kasar ke fama da shi.

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi
Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sissi REUTERS/Carlo Allegri
Talla

Kai tsaye a yanzu asusun bada lamunin zai mikawa Masar dala biliyan 2 da miliyan 75, sannan daga baya ya mika ragowar kudin idan gwamnatin kasar ta yi kyakkyawan amfani da kashin farkon.

Shugabar Asusun IMF Christine Lagarde ta bayyana fatan ganin bashin kudin ya taimakawa Masar shawo kan koma bayan tattalin arzikin da take fuskanta.

Masar ta jima tana fafutukar jawo hankalin masu zuba hannun Jari a kasar, tun bayan rikicin da ta yi fama da shi a 2011, wanda ya jawo kawar da mulkin shugaban kasar Hosni Mubarak.

A satin da ya gabata gwamnatin kasar ta rage darajar kudinta da kashi 50 kan dala, tare da kara yawan kudin ruwa da bankuna ke karba daga kashi 11 zuwa 14, duk domin cika sharuddan da asusun IMF ya kafa mata kafin bata bashin.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.