Isa ga babban shafi
Masar

An hana wa mutanen Masar yin zanga-zanga

‘Yan Sandan kwantar da tarzoma da motocinsu masu silke sun cika titunan birnin Al-Kahira na Masar, a wani mataki na dakile zanga-zangar da al’ummar kasar suka shirya gudanarwa don nuna adawa da matakan tafiyar da tattalin arzikin kasar.

'Yan Sanda sun mamaye dandalin Tahrir domin harmata gudanar da zanga-zanga a birnin Al Kahira
'Yan Sanda sun mamaye dandalin Tahrir domin harmata gudanar da zanga-zanga a birnin Al Kahira REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Rahotanni sun ce kimanin mutane 130 ‘Yan sanda suka cafke da suka fara kaddamar da zanga-zangar.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata kungiyar da ta kira kanta Movement of the Poor ta bukaci al’ummar Masar su fantsama kan tituna a yau Juma’a domin nuna adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da ke ci gaba ta tsananta.

Tun a cikin watan Agustan da ya gabata ne, kungiyar ta kira zanga-zangar, amma sai a cikin makon jiya sakonta ya fi mamaye shafukan sada zumunta na Intanet bayan hukumomin kasar sun kara farashin man fetir.

Hukumomin kasar dai sun dauki matakin ne don nemawa takardar kudin daraja a kasuwannin hada-hada, abin da ya faranta ran bankunan kasar yayin da kuma talakawa ke adawa da matakin saboda tunanin cewa, su za su kwan a ciki.

Jami’an tsaron na Masar sun mamaye dandalin Tahrir da motocinsu masu silke, tare da tanadar barkonan tsohuwa don tarwatsa mutanen da za su fito.

Kazalika hukumomin kasar sun rufe tashar jirgin kasa ta Sadat don hana masu zanga-zangar isa dandalin na Tahrir.

Baya ga birnin Alkahira, haka ma an dauki matakan tsaro a biranen Alexandria da Suez da kuma Minya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.