Isa ga babban shafi
Guinea Bisau

An tarwatsa masu zanga-zanga a Guinea Bissau

Daruruwan mutane ne suka shiga zanga zanga a kasar Guinea Bissau don ganin an sake gudanar da zaben shugabancin kasar, yayin da kungiyar ECOWAS ke kokarin ganin an aiwatar da wata yarjejeniyar shekara guda da za ta magance rikicin siyasar kasar.

Daruruwan jama'a ne suka shiga zanga-zanga don ganin an sake gudanar da zaben shugabancin kasar Guinea Bissau
Daruruwan jama'a ne suka shiga zanga-zanga don ganin an sake gudanar da zaben shugabancin kasar Guinea Bissau AFP
Talla

Masu zanga zangar dauke da alluna daban-daban da ke dauke da rubuce rubuce, sun yi tattaki zuwa fadar shugaban kasar da ke Bissau kafin 'yan sanda su tarwatsa su.

Kasar Guinea Bissau ta yi ta fama da juyin mulki har sau 9 tun shekarar 1980, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke cewa, rashin magance rikicin kasar na iya bai wa masu safarar kwayoyi damar karbe mulki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.