Isa ga babban shafi
Najeriya

Bankin raya Afrika ya amince ya ba Najeriya rancen $600m

Bankin raya Afrika ya amince ya ba Najeriya rancen kudi dala miliyan 600 domin taimakawa shugaba Muhammadu Buhari magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke fuskanta.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban Bankin raya Afrika  Akinwunmi Adeshina
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da Shugaban Bankin raya Afrika Akinwunmi Adeshina thenewsnigeria
Talla

Bankin na AFDB ya ce wannan mataki na farko ne daga cikin adadin kudi dala biliyan daya da Najeriya ke neman rance domin cike gibin kasafin kudinta na bana.

Wannan na zuwa a yayin da Majalisar dattijai ta yi watsi da bukatar Buhari na ciyo bashin kudi dala biliyan 30 daga waje domin gudanar da ayyukan gwamnatin shi a cikin shekaru uku.

‘Yan Majalisar sun yi watsi da bukatar ne saboda rashin gamsassun bayanai akan dalilin cin bashin.

Kodayake shugaban ya ce zai sake aikawa da bukatar zuwa Majalisa domin sake diba bukatar ciyo bashin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.