Isa ga babban shafi
Afrika

Kisan Giwaye na janyo wa Afrika hasara

Wani sakamakon bincike ya ce kisan Giwaye na janyo wa nahiyar Afrika hasarar kudaden shiga daga bangaren yawon bude.

Ana fataucin hauren Giwa daga Afrika zuwa kasashen waje
Ana fataucin hauren Giwa daga Afrika zuwa kasashen waje Reuters
Talla

Binciken ya ce Afrika na iya samun bunkasar tattalin arziki da ya kai dala miliyan ashirin da biyar duk shekara a fannin yawun bude muddun aka dai na kashe giwayen da ake safararsu daga zuwa Turai

Tawagar masana da suka gudanar da binciken sun yi amfani da alkaluma na yawan mutanen da ke zuwa yawon bude ido a kasashen Afrika a duk shekara inda aka gano cewa da dama daga cikinsu sun fi sha’awar ziyarar gidajen namun daji da ake da Giwaye.

Binciken ya ce tsakanin shekarar 2007 zuwa 2014 an sami raguwar Giwaye da kusan kashi talatin cikin dari a nahiyar Africa al’amarin da ya sa aka samu karancin baki ‘yan yawon bude ido da ziyara a nahiyar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fargabar karewar Giwaye a Afrika matukar aka ci gaba da farautar haurensu.

Akalla dala miliyan dari shida ake samu daga fasakwaurin hauren giwa a duk shekara sai dai wannan binciken ya nuna cewa hana farautar Giwaye da kuma safarar haurensu zai kara bunkasa tattalin arzikin kasashen nahiyar Afrika musanman bangaren yawon bude ido.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.