Isa ga babban shafi
Chadi-Kamaru

Idriss Deby Itno ya gana da Paul Biya na Kamaru

Kasar Chadi na kokarin sake farfado dama karfafa dangantakar ta da Kamaru inda yanzu aka bayyana cewa Shugaban Chadi Idris Derby Itno na Yaounde na kasar Kamaru a wata ziyarar rangadin sada zumunci wajen takwaransa na Kamaru Paul Biya.

Idriss Deby Itno Shugaban kasar Chadi
Idriss Deby Itno Shugaban kasar Chadi REUTERS
Talla

Bayanai na cewa yayin wannan ziyara ta kwanaki biyu shugabannin biyu zasu tattauna gameda lamurra da dama da suka shafi tsaro,tattalin arziki tareda yin bitar zantukan Diflomasiya tsakanin Chadi da Kamaru.

Kasashen biyu na daga cikin kasashen dake yakar kungiyar Boko Haram.

Wannan ziyara na zuwa ne adaidai wani lokaci da alummar kasar Kamaru ke juyayin asarar rayyukan mutane da aka samu a hatsarin jirgin kasa na makon jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.