Isa ga babban shafi
Afrika ta kudu

Gwamnatin Zuma na kokarin ceto bangaren ilimi a kasar

A Afrika ta kudu ,sama da dalibai 2000 ne 'yan Sanda suka tarwatsa a wata zanga –zangar nuna bacin ran su ga wanan sabon shiri na kara kudaden shiga jami’a a kasar.Tun a tsakiyar watan Satumba ne Gwamnati ta dau wanan mataki da ya hadu da fushin dalibai. 

'Yan Sanda a Afrika ta kudu sun tarwatsa masu zan-zanga
'Yan Sanda a Afrika ta kudu sun tarwatsa masu zan-zanga REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

A ranar laraba da ta gabata Ministan kudin kasar Pravin Gordan ya sheida cewa Hukumomin za su yi iyakacin kokarin su wajen kawo karshen wannan bore daga dalibai, Ministan dake magana a zauren Majalisar kasar a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin kasar ya bukaci ganin yan Majalisun sun kawo na su gundunmuwa domin samo bakin warware zaren rikicin.

Yanzu haka ana bayyana cewa duk da kokarin magance matsallar ilimi a wannan kasa ana cigaba da samu daliban dake fuskantar matsalloli wajen biyan kudaden karatu a jami’a duk da alkawuran da wasu daga cikin manyan biranen kasar irin su Pretoria suka dau na daukar nauyi biyan karatu wasu dalibai dama tallafa masu da wani dan karami bashi wanda bai taka kara ya kariya ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.