Isa ga babban shafi
Birds

Akwai Tsuntsaye da ke rayuwa a sama

Wani binciken masana kimiya ya gano wasu nau'in tsuntsayen da ke shafe tsawon watanni 10 a sararin samaniya ba tare da sun sauka a doran kasa ba.

Nau'in tsuntsayen na shafe tsawon watanni 10 a sararin samaniya
Nau'in tsuntsayen na shafe tsawon watanni 10 a sararin samaniya Wikipedia
Talla

Binciken wanda aka wallafa a mujallar nazarin halittu ta Amurka ya gasgata hasashen da wani dan Birtaniya mai suna Ron Lockley ya fara yi shekaru 46 da suka shude, in da ya ce, wadannan tsuntsaya da ake kira Common Swift na gudanar da kusan dukkannin rayuwarsu a samaniya.

Anders Hedenstrom, masanin kimiyya a jami’ar Lund da ke Sweden, ya ce idan wadannan tsuntsayen suka yi balaguro daga inda suke sheka na asali a cikin watan Agusta don yin hijira zuwa manyan gandayen daji a yankin tsakiyar Afrika, ba za su sake sauka doran kasa ba har sai sun dawo gida bayan watanni 10, wato lokacin da aka shiga sabuwar kaka.

Mista Hedenstrom ya kara da cewa, wani lokaci, tsuntsayen kan yada zango a shekar tsunsaye don samun hutu da dare, amma fa da dama daga cikinsu ba su taba sauka kasa a cikin tsawon watanni 10.

Tsuntsayen dai na cafkar abinci ne a dai dai lokacin da suke kai-kawo a sararin samaniya kamar yadda binciken ya nuna.

Masana kimiyar sun kara da cewa, duk da babu cikakken bayani kan yadda tsuntsayen ke samun barci, amma ana zaton suna rintsawa ne a yayin da suka nausa can sararin samaniya a kowace rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.