Isa ga babban shafi
Najeriya

Yawan ‘Yan Najeriya da ke ratsa tekun Bahrum zuwa Turai ya karu

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ‘yan Najeriya kimanin 83 ne a kullum ke yin kasadar ratsa tekun Bahrum domin tsallakawa zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci.

'Yan Najeriya na bi ta Agadez a Nijar zuwa Libya su tsallaka tekun Bahrum  zuwa Turai
'Yan Najeriya na bi ta Agadez a Nijar zuwa Libya su tsallaka tekun Bahrum zuwa Turai REUTERS
Talla

Alkaluman da kungiyar ta fitar a wani rahotonta sun nuna cewa, ‘yan Najeriya 22,500 ne suka shiga Turai ta barauniya hanya tun daga watan Janairu zuwa Satumban bana.

Adadin na watanni 9 ya zarce yawan ‘Yan Najeriya 23,000 da suka ratsa tekun Bahrum zuwa Turai a shekarar 2015

Rahotan ya bukaci gwamnatin Najeriya ta yi kokarin habbaka tattalin arzikinta domin magance matsalar talauci, da ke sa ‘Yan kasar yin kasadar tsallakawa zuwa Turai da nufin samun rayuwa mai inganci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.