Isa ga babban shafi
ICC

ICC ta bukaci tattaunawa da Afirka kan janye wakilcin su daga kotun

Kotun Hukunta manyan laifufuka ta bukaci tattaunawa da kasahsen Afirka da ke shirin janye wakilcin su dan ganin an samu fahimtar juna.

Alkalan Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague
Alkalan Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague © ICC-CPI
Talla

Shugaban Majalisar kasahsen da ke da wakilci a kotun, Sidika Kaba ya ce bukatar hakan ya biyo bayan yadda ake bukatar aiwatar da gaskiya da adalci musamman kan laifufukan da ake aikatawa.

Shima Sakatare Janar an Majalisar dinkin Duniya, Ban Ki Moon ya bayyana takaicin sa da shirin Afirka takudu na janyewa daga kotun.

Kasashen Afrika na kalubalantar, ICC, kan mayar da hankali kan shugabanni Afirka kawai a duk tuhume-tuhumen ta, tare da bayyana kotun a matsayin kare farautar kasashen yammaci kan Afirka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.