Isa ga babban shafi
ICC

Gambia ta janye daga kotun ICC

Kasar Gambia tabi sahun wasu kasashen Afirka wajen janyewa daga kotun hukunta manyan laifufuka saboda abinda ta kira yadda kotun ke cin zarafin 'Yan Afirka.

Babbar mai shigar da karar a ICC, Fatou Bensouda, wacce 'yar kasar Gambia ce ta fuskanci koma baya
Babbar mai shigar da karar a ICC, Fatou Bensouda, wacce 'yar kasar Gambia ce ta fuskanci koma baya AFP / Daniels Evert -Jan
Talla

Ministan yada labaran kasar Sheriff Bojang ya shaidawa al’ummar kasar ta kafar talabijin cewar, an kafa kotun ne dan musgunawa 'Yan Afirka musamman shugabanin su, yayin da kotun ke kauda kan ta kan 'yan kasashen Turai da suka aikata laifufuka.

Ministan ya yi misali da tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair wanda kotun taki tuhuma a kan yakin Iraqi.

Bojang ya ce akwai kasashen yammacin duniya akalla 30 da suka aikata laifufukan yaki amma babu guda da aka gurfanar.

Kasar Gambia ta dade tana kokarin ganin kotun ta hukunta kungiyar kasashen Turai kan mutuwar dubban 'yan Afirka da ke mutuwa a teku amma abin ya ci tura.

Wannan dai ba karamar koma baya bane ga Babbar Mai Gabatar da karar kotu Fatou Bensouda wadda 'yar kasar ta Gambia ce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.