Gungun 'yan fashi a Somalia sun saki matukan Jiragen ruwa 26
Rahotanni daga Somalia sun ce, gungun masu fashi a teku sun saki matukan jiragen ruwa 26 da suka kama tare da tsare su tun a shekara ta 2012 tsibirin Seychelles da ke dab da kasar Madaskascar.
Wallafawa ranar:
Matukan Jiragen ruwan duka 'yan nahiyar Asia ne, daga kasashen China, Philippines, Cambodia, Indonesia, Vietnam da kuma Taiwan.
Matukan da suka tsallake rijiya da baya sune mafi dadewa a jerin wadanda ‘yan fashin tekun suka tsare a Somalia.
Matsalar fashi a teku na daya daga cikin abinda ke ciwa Somalia tuwo a kwarya, fama fama da matsalar hare-haren kungiyar al Shabab mai rajin kafa gwamnatin Musulunci a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu