Mutane 52 ne suka mutu a tarzomar kasar Habasha
Rahotanni daga kasar Habasha na cewa mutane da dama ne suka rasa rayyukansu, sakamakon turmutsitsin da ya faru, a lokacin da ‘yan sanda suka yi amfani da harsasan roba domin tarwatsa tarzoma da barke a gefen wasu bukukuwan gargajiya da ‘yan kabilar Oroma suka yi a kasar a wannan lahadi.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An dai gudanar da bukukuwan ne da ake kira Irrecha a wani gari mai suna Bishoftu kamar dai yadda aka saba domin murnar girbe amfanin gonar bana, kuma kamar yadda gwamnan lardin da lamarin ya faru ke cewa, mutane 52 ne suka rasa rayukansu.
To sai dai 'yan adawa sun ce wadanda suka mutu sun fi mutane dari daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu