Congo ta zargi Amurka da haddasa mata rikici
Gwamnatin Jamhuriyar Demokiradiyar Congo ta zargi Amurka ta kitsa tashin hankali a cikin kasar, bayan ta sanya wa wasu manyan jami’an shugaba Joseph Kabila takunkumi.
Wallafawa ranar:
Ministan yada labaran kasar Lambert Mende ya ce, matakin da Amurka ke dauka a kasar ya yi kama da wanda ta dauka wajen jefa kasashen Libya da Sudan cikin rikicin da ke neman hallaka al’ummar kasashen biyu.
Ita dai Amurka ta sanya wa kwamandan sojin kasar Janar Gabriel Amisi Kumba da shugaban 'yan sanda janar John Numbi takunkumi ne saboda yadda jami’an tsaro ke kashe 'yan adawar da ke neman ganin an gudanar da zabe a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu