Isa ga babban shafi
DR Congo

Jean Pierre Bemba ya daukaka karar hukunci shekaru 18 a gidan yari

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Congo, Jean Pierre Bemba da kotun duniya ta daure shekaru 18 a gidan yari saboda samun sa da laifufukan yaki ya daukaka kara, inda yake cewa shari’ar da ake masa na dauke da kura kurai.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Congo Jean Pierre Bemba
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Congo Jean Pierre Bemba REUTERS/JERRY LAMPEN/Pool
Talla

Lauyoyin da ke kare shi, sun ce an gabatar da karar ne ranar 19 ga watan nan, inda suke cewa an ci zarafin sa lokacin wanda ke nuna cewar an ci zarafin sa.

Kotun ta samu tsohon mataimakin shugaban kasar da laifin sanya yara kanana aikin soji, fyade, cin zarafin Bil Adama da kuma hallaka mutane da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.