Isa ga babban shafi
Sudan

Amnesty ta ce Sudan na amfani da Makami mai Guba a Darfur

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Sudan da kashe dimbin fararen hula, cikin su harda yara kanana wajen amfani da sinadari mai guba a Darfur.

Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir
Shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Rahotan kungiyar ya ce an kai irin wadannan hare hare sama da 30 a kauyuka dabam dabam a Yankin Jabel Marra da ke Darfur tsakanin watan Janairu zuwa Satumba na wannan shekarar.

Kungiyar ta ce tsakanin mutane 200 zuwa 250 suka mutu sakamakon harin cikin su harda kananan yara da mata.

Kungiyar ta kuma zargi kai munanan hare haren bama bamai kan fararen hula da kuma yiwa mata fyade, abin da jami’ar ta Tirana Hassan ta bayyana a matsayin laifufukan yaki.

Gwamnatin Sudan ta yi watsi da rahotan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.