Giwaye sun ragu sosai a nahiyar Afrika
Taron masana harkar kula da gandun daji na duniya ya ce, an samu raguwar giwayen da ke nahiyar Afrika sosai a cikin shekaru 10 da suka gabata, in da kididdiga ta nuna cewar, akalla giwaye dubu 111, aka kashe don sayar da haurensu.
Wallafawa ranar:
Wannan dai shi ne adadi mafi tayar da hankali da aka samu cikin shekaru 25 a wajen taron masanan da aka yi a kasar Afrika ta kudu don samo hanyar kare dabbobin.
Kasashen Namibia da Zimbabwe, sun yi Allah-wadai da dokar da manyan kasashen duniya suka kafa ta hana su sayar da hauren giwayen, wadda ministan muhallin Zimbabwe, Oppah Muchinguri ya bayyana a matsayin ci gaba da mulkin mallaka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu