Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Congo

Ana zargin Shugaban Congo Sassou Nguesso da kisan fararen fula

Wasu gungun kungiyoyin siyasa tareda hadin guiwar kungiyoyi masu zaman kansu a Jamhuriyar Congo sun fitar da wani sakamakon bicinke dake nuni cewa sama da mutane 100 ne suka rasa rayukan su, kama daga lokacin zaben raba gardama na kasar zuwa babban zabe da ya baiwa Shugaban kasar kuma dan takara a lokacin Denis Sassou Nguesso nasarar lashe zaben.

Shugaban Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso
Shugaban Congo Brazzaville Denis Sassou-Nguesso REUTERS/Anis Mili
Talla

Wadannan kungiyoyi sun aike da sakamako zuwa MDD, dama Kotun hukunta mayan laifuka da hurumin gani wadannan hukumomin sun dau matakan da suka dace domin gaskiya ta bayyana.

Kungiyoyin kasar na zargin rundunar tsaro ta fadar Shugaban kasar da hannu a wannan kazamin aiki, sai dai Ministan shari’ar kasar Pierre Mabiala ya sheidawa gidan rediyon Faransa sashen faransanci cewa neman shafawa shugaban kasar kashin kaji ake kokarin cimma.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.