Isa ga babban shafi
DRC

Mutane 10 sun rasa rayukansu a Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo

Mutane 10 sun rasa rayukansu a Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Kongo, sakamakon fadan da aka gwabza a birnin Kananga da ke tsakiyar kasar.

Jami'an tsaron Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo cikin shirin ko ta kwana
Jami'an tsaron Jamhuriyyar Dimokaradiyyar Congo cikin shirin ko ta kwana REUTERS/Stringer
Talla

Jami’an tsaro dai sun maida martini kan harin daukar fansa, da ‘yan tawaye suka kai musu game da kashe jagoransu da hukumomin tsaron jamhuriyyar Dimokaradiyar Kongon suka yi, a watan Agusta.

Mayakan dai sun kai harin ne kan filin jiragen sama na birnin Kananga, inda Ma’aikacin jirgi guda ya rasa ransa.

Jamhuriyyar Congo ta shafe shekaru tana fama da rikici sakamakon rashin daidaiton siyasar kasar, sai kuma fama da hare-haren 'yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.