Isa ga babban shafi
Najeriya

Aero ya dakatar aiki a Najeriya

Katafaren Kamfanin sufurin jiragen sama Aero Contractors a Najeriya ya sanar da dakatar da ayyukansa a kasar da kuma tura daukacin ma’aikatansa hutun dole daga yau daya ga watan Satumba.

Kamfanin AERO Contractors a Najeriya
Kamfanin AERO Contractors a Najeriya dailypost
Talla

Shugaban kamfanin Fola Akinkuotu ya ce sun dauki matakin ne don nazarin halin da ake ciki da kuma sake dabarun yadda za su inganta kamfanin wajen samun riba.

Jami’in ya danganta matakin da halin da tattalin arzikin Najeriya ya samu kansa a yau, al’amarin da ya ce zai tilastawa wasu kamfanonin jiragen sama dakatar da ayyukansu ko ficewa daga Najeriya.

Kamfanin Aero na cikin manyan jiragen da ke jigilar fasinja a sassan Najeriya kuma ya dakatar da aiki ne saboda rashin samun riba.

Jirage dai na fama da matsalar karancin man da jirage ke amfani da shi a Najeriya, matakin da ya haifar da karancin fasinja sakamakon farashin jirgin da ya yi tsada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.