Isa ga babban shafi
Najeriya

"Makwanni ya rage wa Boko Haram"

Rundunar sojin Najeriya da ke fada da Boko Haram, ta ce nan da ‘yan makonni kadan za ta murkushe illahirin mayakan kungiyar tare da dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sanye da kakin Soja
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari sanye da kakin Soja STRINGER / AFP
Talla

Babban kwamandan da ke jagorantar ayyukan fada da ‘yan kungiyar Janar Lucky Irabor, ya ce a halin yanzu ‘yan Boko Haram na killace ne a wasu ‘yan wurare da ke cikin gandun dajin Sambisa.

Boko Haram ta shafe shekaru bakwai tana kai hare hare a Najeriya, kuma har yanzu mayakan na ci gaba da zama barazana a yankunan da ke kewaye da tafkin Chadi na Najeriya da Kamaru da Nijar da kuma Chadi.

Babban Kwamandan ya ce babu sauran wani yanki da Boko Haram ke iko illa kauyuka guda biyu na Abadan da Malanfatori da ke kusa da tafkin Chadi.

Janar Irabor ya ce yanzu haka suna shirin kaddamar da wani sabon farmaki a Dajin Sambisa bayan sun jinkirta sakamakon ruwan sama da aka tafka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.