Bakin-Haure
An ceto bakin haure 6,500 a Teku
Duk da hadarin da tafiya Turai ci rani ke da shi da yadda dubban mutane ke rasa rayukan su wajen nitsewa a teku, hakan baya hana mutane neman ganin sun ratsa tekun ba.
Wallafawa ranar:
Talla
Jami’an tsaron gabar tekun Italiya sun ce a jiya litinin kawai sun ceto kananan jiragen ruwa mai dauke da baki 6,500, cikin su harda wani karamin kwale kwalen kamun kifi mai dauke da mutane 700 da aka cunkusa a ciki.
Majalisar Dinkin Duniya tace a cikin watanni 8 da suka gabata, an ceto baki 112,500 dake neman zuwa Turai, banda daruruwa da suka rasa rayukansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu