Isa ga babban shafi
Afrika-Japan

Afrika da Japan sun kulla yarjejeniyar kasuwanci da cinikayya

A karshen taron yini biyu da aka gudanar tsakanin Afrika da Japan a birnin Nairobin Kenya, ‘yan kasuwa da kuma kamfanoni daga bangarorin biyu, sun kulla yarjeniyoyin guda 73 da suka shafi kasuwanci da cinikayya.

Firaiyi ministan Japan Shinzo Abe da sauran shugabanin kasashen Afrika a birnin Nairobin Kenya.
Firaiyi ministan Japan Shinzo Abe da sauran shugabanin kasashen Afrika a birnin Nairobin Kenya. Reuters/路透社
Talla

Yarjeniyoyin sun ta’allaka ne a kan ciniki da kuma sarrafa danyar hajar da kamfanonin Japan za su saya daga nahiyar Afirka acewar firaministan Japan Shinzo Abe da kuma shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.

Shugaban Uhuru Kenyatta ya ce alaka tsakanin Japan da Afirka, wata dama ce domin habaka tattalin arzikin nahiyar, ta hanyar fitar da danyar hanja wadda kamfanonin Japan ke matukar bukata.

A tsawon kwanaki biyu, firaministan na Japan da kuma shugabannin wasu kasashe na Afirka akalla talatin, sun cimma matsaya kan yadda za a inganta sha’anin kiwon lafiya, tsaron, samar da hanyoyi da kuma makamashi, da kuma yadda Japan za ta taimakawa nahiyar domin samun nasara a wadannan fannoni.

Wannan ne dai karo na shida da aka shirya irin wannan taro a tsakanin bangarorin biyu, inda a wannan karo Bankin Duniya ya shigo domin bayar da tasa gudunmuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.