Isa ga babban shafi
Zimbabwe

'Yan sanda sun hana gangamin gamayyar Jam'iyyun adawa

‘Yan sandan kwantar da tarzoma a Zimbabwe sun sake yin amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma duka da kulake, domin hana dandazon masu zanga zanga isa filin da ‘yan adawa suka shirya gangami.

Zanga zangar adawa da gwamnatin Robert Mugabe
Zanga zangar adawa da gwamnatin Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Gangamin da jam’iyyun adawar kasar suka shirya yi, ya samu amincewar wata kotu a kasar, kuma babban makasudinsa shi ne tursasawa Mugabe awaitar da kwaskwarima da aka yiwa dokokin zaben kasar kafin shekara ta 2018.

‘Yan adawa a Zimbabwe na fafutukar ganin Robert Mugabe mai shekaru 92 ya sauka daga mukaminsa bayan shafe sama da shekaru 35 yana mulkin Zimbabwe.

Tun a lokacin da Mugabe ya bayyana aniyar sake zarcewa bisa shugabancin kasar ne ya fara fuskantar turjiya daga ‘yan kasar ciki harda wadanda suka yi gwagwarmayar neman 'yancin kasar tare.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.