CBN ta dakatar da bankuna 9 daga cinikin kudaden waje
Babban Bankin CBN ya dauki matakin dakatar da wasu bankuna 9 daga cinikin kudaden waje saboda rawar da suka taka na kin mayar da kudaden gwamnati da ya kai sama da Dala biliyan 2.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Bayanai sun ce bankunan sun ki mayar da kudaden kamfanin man kasar na NNPC ne zuwa asusun gwammatin tarayya kamar yadda gwamnatin ta bada umurni.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki sakamakon faduwar darajar Naira.
Bankunan da al'amarin ya shafa sun hada da UBA da Fidelity da Diamond bank sai FCMB da Sterling bank da kuma Heritage bank sauran sune Keystone da Skye bank da kuma First Bank.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu