Isa ga babban shafi
Habasha

Ambaliyar ruwa ta raba dubunnan mutane da gidajensu

Majalisar dinkin duniya ta ce a kalla ‘yan kasar Habasha 600,000 suka tsere daga gidajensu a watan Mayu da ya gabata saboda ambaliyar ruwa.

Barazanar ambaliyar ruwa a Habasha
Barazanar ambaliyar ruwa a Habasha RFI
Talla

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya na zuwa ne yayinda a gefe guda masu hasashen yanayi ke gargadin samun karin zubar ruwan sama a watan Disamba mai zuwa a kasar.

Sai dai kuma rahoton ya kara da cewa kawo yanzu, da wasu daga cikin wadanda ambaliyar ruwan ta daidaita sun dawo gidajensu amma cikin bukatar taimakon gaggawa na abinci da magunguna.

A shekara ta 2015 kasar Habasha ta fuskanci fari mafi muni a tarihi, wanda ya jefa a kalla mutane miliyan 10 cikin yunwa kuma basu samu sauki hakan ba sai a watan Maris da ya gabata bayan fara saukar ruwan sama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.