Isa ga babban shafi
Mauritania

An yankewa mutane 13 hukuncin zaman yari na shekaru 15

Wata kotun wucin gadi a kasar Mauritania yankewa mutane 13 ‘yan kungiyar yaki da bautar da mutane ta IRA da ke kasar hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 15.

Masu zanga zangar adawa da bautar da mutane a Mauritania
Masu zanga zangar adawa da bautar da mutane a Mauritania SEYLLOU / AFP
Talla

An dai yankewa mutanen wannan hukunci ne saboda samunsu da laifin haddasa tarzoma yayin gudanar da wata zanga zanga a kasar cikin watan Yunin da ya gabata kamar yadda masu gabatar da kara suka bayyana.

Sai dai kuma wadanda aka yankewa hukuncin sun kafe kan cewar ana yi musu bita da kulli ne na siyasa, domin a cewarsu, basu halarci wajen da aka gudanar da zanga zangar ba.

A cewar Sarah Mathewson, mai kula da shirye shiryen Kungiyar yaki da bautar da mutane ta Duniya, gwamnatin Mauritania tana kokarin dakile kyakkyawar manufar ‘ya’yan kungiyar na kawo karshen bauta a kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.